Koma Labarai
Labarai

Taɓarɓarewar shugabanci da ake fama da shi na da alaƙa da rashin kishin ƙasa a Najeriya - Baba Maje

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Taɓarɓarewar shugabanci da ake fama da shi na da alaƙa da rashin kishin ƙasa a Najeriya - Baba Maje

Wani dattijo mai Kimanin shekaru 69 a duniya mai suna Usman Baba Maje, ya ce inda shugabannin Najeriya na koyi da magabata da ƙasar ba ta shiga halin da take ciki ba.

Dattijon ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ƴancin kai, da ake gudanarwa yau Alhamis 1 ga watan Oktoba, 2026.

A cewar sa, "A gaban mu gimbiya Elexendarer Margeret, ta danƙa amanar Najeriya a hannun su Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, kuma sun sauke nauyin," in ji Baba Maje.

Ya kuma bayyana cewar taɓarbarewar shugabanci da ake fama da shi yanzu na da alaƙa da rashin kishin ƙasa.

A cewar sa, "Matasa su ne za su iya kawo sauyi ta hanyar zaɓo nagartattun shugabanni domin matasan su ne masu zaɓe," in ji Baba Maje.

Ya kuma ƙara da cewa, Najeriya ƙasa ce mai tarin arziki amma wasu yan tsirarun mutane ne ki sarrafa arzikin kasar, kuma ba haka ya kamata a samu ba.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Dattijon ya bayyana cewar da za gwada nauyin shugabanni na yanzu da na baya, za a ga cewar tamkar buhun kowar wake ne da na gero.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM