Har yanzu ba a bayar da umarnin cire jar hula ba a jira lokaci - Gwamnatin Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa har yanzu ba a bayar da umarnin cire jar hula a jihar ba.
Wannan na cikin sanarwar da Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafin sa na sada zumunta.
Ya ce shigar da aka ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi ba tare da har hula ba, wannan wata fita ce ta musamman da aka yi a Yola ta Jihar Adamawa, da manyan baƙi su ka yi anko.
Sanarwar ta kuma ce kan batun cire jar hular a jira, domin komai akwai lokaci.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ankon da gwamnan su ka saka a Yola, ta jawo cece-kuce musamman ma a shafukan sada zumunta, inda wasu suka rinƙa yaɗa cewar Abba Kabir, ya cire jar hula.



