Macky Sall ya janye takararsa ta neman Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tsohon shugaban ƙasar Senegal, Macky Sall, ya janye takararsa ta neman zama Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan wata ƙuri’ar tantance goyon baya da mambobin Kwamitin Tsaro suka gudanar ba bisa ƙa’ida ba ta ƙarshe, wanda ya nuna cewa bai samu isasshen goyon baya ba.
Sai dai Macky Sall ya sanar da matakin nasa ne bayan ƙuri’ar tantance goyon bayan ’yan takarar da Kwamitin Tsaro ya gudanar a ranar 16 ga Oktoba, domin tantance waɗanda ke neman maye gurbin António Guterres a matsayin Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.
A cikin wata sanarwa, tsohon shugaban na Senegal ya ce ya tuntubi shugaban ƙasar Burundi, Évariste Ndayishimiye, da shugaban Senegal na yanzu, Bassirou Diomaye Faye, kafin ya yanke shawarar janye takararsa.
Kafar DCL ta ruwaito cewa, Janyewar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tantance ’yan takarar da za su iya maye gurbin António Guterres a shugabancin Majalisar Ɗinkin Duniya.



