Rashin wadatacciyar magudanar ruwa na kawo ambaliyar ruwa a yankin mu - Mazauna Ɗorayi a Kano

Al'ummar unguwar Ɗorayi bayan gidan sarkin Dutse a ƙaramar hukumar Gwale a Kano, sun gudanar da taron addu'a tare da neman taimakon gwamnatin jihar Kano, da kuma shugabancin ƙaramar hukumar su, da da su kai musu ɗauki bisa barazanar ambaliya da ke damun su sakamakon rashin magudanar ruwa.
Limamin masallacin Salafussalih da ke unguwar Ɗorayi Ƙarama Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ne ya jagoranci taron addu'ar jim kaɗan bayan idar da sallar juma'a, inda ya miƙa koken su ga mahukunta domin ganin an kai musu ɗauki.
Mallam Ibrahim Bunkure, ya ce sun daɗe suna bibiyar mahukunta domin ganin an samar musu da babbar magudanar ruwa amma kawo yanzu lamarin ya ci tura, a don haka suke kira da a kai musu ɗauki.
Suma wasu mata da ke zaune a unguwar sun nuna damuwar su kan lamarin, inda suka ce a duk lokacin da suka ga hadari ya taso, sakamakon rashin samun sukunin inda za su zauna suna shiga cikin damuwa.
"A duk lokacin da aka yi ruwan sama mai yawa ƴan shiga cikin ɗakunan mu sakamakon rashin ƙarancin magudanar ruwan da muke fama da shi a cikin unguwar mu tare da gaza yin bacci a irin wannan lokacin saboda fargabar da muke shiga," in ji su.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya'u ya ruwaito cewa, mutanen unguwar dai sun ce sun haura shekaru 20 a wannan hali da suke ciki, tare da bayyana cewa sun yi duk iya ƙoƙarin su don magance wannan matsalar amma kawo yanzu shiru.



