Kano ta zama kan gaba wajan yaƙi da sauyin yanayi - Ministan Muhalli

Gwamnatin Tarayya ta jinjinawa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarin da take yi wajen dasa itatuwa da farfaɗo da muhalli, yana mai cewa jihar Kano ta zama abar koyi wajan yaƙi da sauyin yanayi.
Ministan Muhalli na ƙasa, Balarabe Abbas Lawal, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, lokacin bikin Ranar Great Green Wall ta 2026, wato ƙaddamar da gangamin dashen itatuwa na shekarar 2026, da kuma miƙa ofishin shalkwatar hukumar National Agency for the Great Green Wall (NAGGW) zuwa Kano.
Ministan ya ƙara tabbatar da cewa Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen muhalli a jihar Kano.
A hannu guda kuma, Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano, Dakta Ɗahir Muhammad Hashim, ya ce "mayar da shalkwatar hukumar zuwa Kano babban ci gaba ne ga manufofin muhalli na ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa jihar Kano ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da manufofin sauyin yanayi, in da ta dasa miliyoyin itatuwa tare da farfaɗo da dubban hekta na ƙasar da ta lalace.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da sauran abokan hulɗar ci gaba, domin ƙarfafa ayyukan kare muhalli, da kuma yaƙi da yaɗuwar hamada, da inganta rayuwar al'umma.



