Koma Labarai
Tsaro

Tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta sana'ar sayar da fetur a jarka, da POS, da Cajin waya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta sana'ar sayar da fetur a jarka, da POS, da Cajin waya

Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta saye, da sayarwa, jigila da ajiye man fetur a jarkoki a fadin jihar, tare da rufe sana'ar POS da wuraren cajin waya a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa.

Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar Litinin 15 ga Yuni, 2026.

Sanarwar ta kuma ce Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya amince da sabbin matakan bayan wani taron gaggawa kan tsaro da ya hada hukumomin tsaro, sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki.

"An ɗauki matakan ne domin daƙile ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane, bayan binciken tsaro ya nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da man fetur, POS da wuraren cajin waya wajen gudanar da ayyukansu, in ji sanarwar.”

Gwamnatin jihar ta kuma haramta amfani da babura a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa, domin rage zirga-zirgar masu aikata laifuka a yankunan, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.

Har ila yau,.Gwamnatin ta bukaci al'umma da su bi sabbin umarnin tare da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai, tana mai gargadin cewa ba za ta sassauta wa masu karya dokokin ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM