Mazauna gidajen gyaran hali a Kano, 52 sun fara rubuta jarabawar NECO da NABAIS ta 2026

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar Kano, ta ce wasu mazauna gidajen su 52, maza guda 41, mata 11, sun zauna domin zana jarrabawar kammala makarantar Sakandire NECO, da NBAIS, ta 2026, a wani ɓangare na shiryar da duk mutumin da ke tsare a gidajen tare da samun ingantaccen ilimi.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar a ranar Juma'a 3 ga Yuli, 2026.
Sanarwar ta ce mazauna gidajen sun fara rubuta jarabawar ne ta hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Ƙasa (NECO) da kuma Hukumar Shirya Jarabawar Larabci da Addinin Musulunci (NABAIS), a wani mataki da ke nuna ƙudirin Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya na ci gaba da amfani da ilimi wajen gyara da sake rayar da rayuwar fursunoni.
Sanarwar ta kuma ce daga cikin masu rubuta jarabawar akwai maza 41 da mata 11, waɗanda aka zaɓo daga gidajen gyaran hali daban-daban da ke faɗin Jihar Kano.
Sanarwar ta ce hakan na daga cikin ƙoƙarin hukumar na inganta gyaran hali, sauya ɗabi'a da kuma shirya fursunoni domin komawa cikin al'umma bayan kammala wa'adin zaman da suke yi, ta hanyar ba su damar samun ingantaccen ilimi da koyon sana'o'i.
Shugaban Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya reshen Jihar Kano, CC Yusuf Ahmad Lakpene, ya ziyarci cibiyoyin da ake gudanar da jarabawar domin sa ido kan yadda aka fara gudanar da ita, inda ya bayyana shirin a matsayin wani babban ci gaba wajen cika manufofin gyaran hali da sake farfaɗo da rayuwar fursunoni.
Yayin da yake jawabi ga masu rubuta jarabawar, CC Lakpene, ya buƙace su da su kasance masu ladabi, bin doka da kuma riƙon amana a duk tsawon lokacin jarabawar.
Ya kuma ce ilimi na daga cikin manyan hanyoyin da ke sauya rayuwa, da rage komawar mutum aikata laifi, tare da shiryar da mazauna gidajen su zama 'yan ƙasa masu amfani bayan sun kammala zaman da suke yi a cibiyoyin gyaran hali.
Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa ɗaukar nauyin kuɗin rajistar jarabawar ga mazauna gidajen.
A cewarsa, "Wannan mataki ya nuna yadda gwamnatin ke ba da muhimmanci ga ilimi mai haɗa kowa da kuma bunƙasa jarin ɗan Adam, har ma da waɗanda ke gidajen gyaran halin.
CC Lakpene ya sake jaddada cewa, Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, za ta ci gaba da faɗaɗa shirye-shiryen ta a fagen ilimi a cibiyoyin gyaran hali a matsayin wani ɓangare na dabarunta na ƙarfafa koyo, bunƙasa rayuwar fursunoni da kuma samar da ɗorewar sauyin hali.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a yayin ziyarar, Mai Kula da Hukumar gidajen gyaran halin na Kano, ya samu rakiyar Shugaban da ke kula da gidan gyaran hali na Kurmawa, DCC Ibrahim Isa Rambo, da ACC Musa Muhammad Kibiya, da kuma Shugaban Makarantar ɗaliban da ke karatu a gidajen gyaran hali, DSC Ahmad Muhammad Alkanawi.



