Koma Labarai
Siyasa

PDP ta baiwa tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, takarar gwamna a Gombe.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
PDP ta baiwa tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, takarar gwamna a Gombe.

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya shiga sahun ‘yan takara domin neman kujerar Gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027 a jam’iyyar PDP.

Pantami ya zama ɗan takarar PDP ne bayan sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, matakin da ya ba shi damar tsayawa takara a sabuwar jam’iyyar tasa, kamar yadda kafar DailyTrust ta ruwaito.

Sheikh Pantami dai ya sha kayi a zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a jihar Gombe, da aka gudanar a jam'iyyar APC, lamarin da wasu ke ganin ya taka rawa wajen ficewar sa daga jam'iyyar zuwa PDP.

Ready to PlayDala FM88.5 FM