Koma Labarai
Masarauta

Sarkin Kano ya dakatar da wani Hotel, kan zargin lalata da mata masu ƙananan shekaru a ciki

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Kano ya dakatar da wani Hotel, kan zargin lalata da mata masu ƙananan shekaru a ciki

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya dakatar da Hotal ɗin Stephrica Guest palace, da ke garin Kureƙen Sani wanda ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.

‎Majalisar masarautar Kano ce ta dakatar Hotel, ɗin ƙarƙashin jagorancin Matawallen Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim Matawalle, bayan ƙorafe-ƙorafen al'ummar yankin da suka gabatar a gaban majalisar masarautar Kano.

‎Matawallen Kano Aliyu Ibrahim Matawalle, ya kuma umarci mamallakin Hotel ɗin da ya mayar da ya mayar da shi zuwa Asibiti, ko makaranta domin amfanar al'ummar yankin baki ɗaya.

Tun da farko al'ummar garin na Kureƙen sani da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, sun koka kan yadda wani mutum ya buɗe Hotel din a cikin unguwar bayan da hukumar da ke bada izinin kafa Hotel ta hana shi lasisi, amma sai da ya buɗe inda mutane suka yi zargin ana kai ƙananan yara mata ana lalata da su a ciki.

‎A nasa jawabi bayan dakatar da Hotel ɗin, Shugaban ƙungiyar cigaban cigaban al'ummar garin Kureƙen sani, Malam Muhammad Sabi'u Yahaya, ya godewa masarautar Kano bisa bincike da ta yi a kan Hotel ɗin, don ganin yadda ake shige da fice da ƙananan yara a ciki.

‎Wakilinmu na Masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya ruwaito cewa, a yayin zaman fadar na yau Laraba, majalisar masarautar Kano, ta amince da dawo da dagacin garin Rikadawa da ke ƙaramar hukumar Madobi Malam Rabi'u Yusuf, matsayin sa na dagacin garin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM