Koma Labarai
Labarai

Dagacin Sharaɗa ya jagoranci sulhunta matasa ƴan siyasar yankin kan gujewa siyasar gaba a shafukan sada zumunta.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Dagacin Sharaɗa ya jagoranci sulhunta matasa ƴan siyasar yankin kan gujewa siyasar gaba a shafukan sada zumunta.

Dagacin garin Sharada da ke ƙaramar hukumar Birni a Kano, Alhaji Ilyasu Mu'azu, ya ja kunnen ƴan siyasar Sharada, da su guji sukar junan su a shafukan sada zumunta, don gudun tada tarzoma.

Dagacin ya bayyana hakan ne a yayin taron zaman sulhunta wasu daga cikin ƴan siyasar yankin, da ke sukar junan su a shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa suka samu saɓani.

Zaman sulhun ya gudana ne a fadar dagacin da ke unguwar Sharaɗa, a ranar Lahadi 19 ga Yuli, 2026.

A baya dai kafin zaman sulhun, mafi yawan matasan suna sukar junan su a shafukan sada zumunta, kuma ba kasafai suke magana ba, amma kafin a tashi daga zaman sai da dagacin ya sulhunta su har suka rinƙa wasa da dariya a wajen.

Yayin zaman sulhun, Alhaji Ilyasu Mu'azu Sharaɗa, ya kuma gindaya musu sharuɗan cewar, za su yi siyasa ba da gaba ba, da kaucewa tayar da rikici, su kuma ci gaba da mutunta junan su.

Bayan kammala zaman sulhun, dagacin ya kuma sayawa matasan ƴan siyasar yankin Sharaɗa, Gyaɗa mai ɓawo kowannen su ya tafi yana murna da farin ciki, domin ƙarfafa zumuncin da ke tsakanin su.

Wakilinmu Adam Abubakar Indallahi ya ruwaito cewa, a yayin zaman sulhun, matasan ƴan siyasa na yankunan Sharaɗa da ke da ra'ayin siyasa daban-daban, da dama ne suka halarta.

Ready to PlayDala FM88.5 FM