Koma Labarai
Tsaro

Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wani matashi da ya sare ɗan yatsan hannun sa, saboda za a bashi miliyan 80.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wani matashi da ya sare ɗan yatsan hannun sa, saboda za a bashi miliyan 80.

Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wani matashi da ya sare ɗan yatsan sa na hannu, bayan da aka bashi kwangilar nemo ɗan yatsan domin a bashi Naira miliyan Tamanin, a ƙaramar hukumar Rano.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 09 ga watan Satumba, 2026.

Sanarwar ta ce, tun da farko matashin ya je Ofishin Yan Sanda ne da ke Rano, inda ya shigar da korafi cewa, wani ya ce ya nemo masa dan yatsa na mutum mai rai, zai bashi Naira miliyan 80.

Da ya nemi ɗan yatsan ya rasa shi ne ya samu wuka ya yanke nasa ya bashi, kuma daga baya ya hana shi kuɗin, a don haka ne yake ƙorafi a kan mutumin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM