Kotun tafi-da-gidanka ta REMASAB, ta yanke hukunci ga bankin ECO da gidan man NNPC da wasu gidajen Mai a Kano

Hukumar kwashe Shara da tsaftar Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB) ta ƙara himma wajen aiwatar da dokokin tsaftar muhalli ta hannun Kotunta ta Tafi-da-Gidanka mai kula da laifukan tsaftar muhalli, (Mobile Court), a wani ɓangare na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsafta, da lafiyar al'umma da kuma ingantaccen muhalli mai ɗorewa a faɗin Jihar.
A zaman kotun na baya-bayan nan, an gurfanar da wasu manyan kamfanoni da cibiyoyin kasuwanci bisa laifukan keta dokokin tsaftar muhalli, inda kotun ta same su da laifi tare da yanke musu hukunci bisa tanadin doka.
Wannan na cikin sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar ta REMASAB, Abubakar Ahmad, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata 30 ga Yuni, 2026.
Sanarwar ta ce, daga cikin waɗanda aka samu da laifi akwai ECO Bank da ke France Road a Kano, wanda aka kama da laifin rashin bin ƙa'idojin tsaftar muhalli.
Haka kuma, kotun ta gurfanar da AA RANO Filling Station da ke Bombai Road, da Forte Oil Filling Station da ke kan Murtala Muhammad Way, da NNPC Filling Station da ke kan Club Road, da kuma Taj Mahal Restaurant da ke kan Alu Avenue kusa da Ahmadu Bello Way, da kuma SDY Filling Station da ke kan Club Road.
Kotun ta same su ne da laifuffuka daban-daban da suka haɗa da rashin kula da tsaftar muhalli, da toshe magudanan ruwa, da rashin samar da isassun wuraren zubar da shara, da kuma wasu laifukan da suka saɓa wa dokokin tsaftar muhalli na Jihar Kano.
Bayan kammala shari'ar, Kotun Tafi-da-Gidanka (Mobile Court) ta yanke wa waɗanda aka samu da laifi hukuncin zaman gidan gyaren hali (Correctional Center) na tsawon makonni biyu ko kuma biyan tara, kamar yadda dokokin tsaftar muhalli na Jihar Kano suka tanada.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, da yake jawabi bayan kammala zaman kotun, Manajan Daraktan Hukumar REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, ya sake jaddada kudirin hukumar na tabbatar da tsafta da ingantaccen muhalli a dukkan sassan Jihar Kano.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar Kano, da masu gudanar da kasuwanci da kamfanoni masu zaman kansu da su kasance masu bin dokokin tsaftar muhalli tare da kula da tsaftar muhallansu domin kare lafiyar al'umma da kuma tallafa wa ci gaba mai ɗorewa.
Dr. Khalil ya kuma tabbatar da cewa hukumar REMASAB, za ta ci gaba da aiwatar da dokokin tsaftar muhalli cikin adalci ba tare da nuna son rai ko wariya ba, yana mai gargadin cewa duk wani mutum ko ƙungiya da aka samu da laifin karya dokokin tsaftar muhalli za a gurfanar da shi a gaban kotu tare da ɗaukar matakin da doka ta tanada.



