Gwamnati a rinƙa hukunta duk Alƙali, ko jami'in tsaron da suka saki ɗan daba ba bisa ƙa'ida ba a Kano - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation, ta ce idan har da gaske gwamnatin Kano take wajen yaƙi da faɗan daba a jihar nan, sai ta hana ƴan siyasa yawo da ƴan daba riƙe da muggan makamai wajen harkokin siyasar su.
Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Kwamared Auwal Usman Awareness, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma'a 23 ga Mayu, 2026.
Ya ce tunda an san masu ɗaukar nauyin ƴan daban akwai buƙatar gwamnati da jami'an tsaro su ƙara ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar a Kano.
Kwamared Auwal Usman, ya kuma ce dole gwamnati ta baiwa jami'an tsaro umarni mai tsauri ta yadda za su yi abinda ya dace domin daƙile faɗan daba da Kwacen waya a jihar Kano.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin faɗan daban da ƙwacen waya suka addabi jama'a a sassan jihar Kano, inda suke ci gaba da kira ga mahukunta da su ɗauki mataki don magance matsalolin.
Har ila yau, Kwamared Auwal Awareness, ya kuma buƙaci gwamnatin jihar Kano, da ta rinƙa ɗaukar matakin da ya dace a kan duk Alƙali, ko jami'in tsaron da aka samu da sakaci kan ɗaukar mataki a kan duk wanda aka samu da mu hannu a haddasa rikicin daba a jihar.
"Mafi yawan lokuta sakin ƴan daba da Alƙalai, da kuma jami'an tsaro ke yi, musamman ma da ƴan siyasa ke karɓar su, na taka rawa wajen ta'azzarar harkokin daba a jihar Kano, in ji Auwal.”
A cewar sa, ya kamata Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen magance harkar daba bisa yadda lamarin ke salwantar da rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar.



