Mun shiga tashin hankali bisa fara auna mana gonaki ba tare da an biya mu ba - Mazauna Kuyan a Kano

Mamallaka Gonaki a yankunan Kuyan ta Sidi, da Kuyan ta Inna da kuma Ɗan Jirima da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, sun koka tare da neman ɗaukin gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, kan yadda suka wayi gari da ganin an zo da mota ana auna musu Gonaki.
Mamallaka Gonakin sun ce, auna gonakin nasu da aka zo ana yi ba tare da an tuntuɓe su ba a ranar Litinin, ya matuƙar tayar musu da hankali, domin wasun su ma sun kasa yin bacci, da cin abinci sakamakon halin da suka samu kansu a ciki.
Da yake zantawa da gidan rediyon Dala FM, guda daga cikin mamallaka Gonakin, da awon ya biyo ta gonakinsa biyar, da kuma na marayunsu biyar, Haruna Ya'u, ya ce bayan da suka ga ana auna gonakin nasu ne suka tuntuɓi dagata, da masu unguwannin su, sun ce basu da masaniya a kai.
Ya ce a tunanin su yadda zaɓen 2027, ya taho gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ba zai sanya a yi awon gonaki ba a yanzu, a don haka suke kira a gare shi da ya sa a bincika tare da yi musu adalci a kai.
A cewar sa, "Da mu ka tambaya daga ina aka zo awon, masu aikin sun faɗa mana cewar daga Ma'aikatar ƙasa da tsare-tsare aka turo su, abinda ya ƙara ɗaga mana hankali, kuma mun haura mu dubu biyar masu ƙorafin, in ji Haruna.”
Shima da yake bayyana damuwar sa Ale Basiru Suleman, ya ce awon gonakin nasu da aka zo a na yi ya tayar musu da hankali, bisa yadda ɗan abinda ya rage musu na gonakin nasu biyo bayan awo kusan huɗu da aka gudanar a baya shima aka zo ana aunawa, a don haka ne suke kira da gwamnatin jihar Kano ta shiga cikin lamarin.
Ya kuma ce sau biyar ke nan awo yana biyo wa ta kadarorin su a yankunan nasu, sai gashi ɗan abinda ya rage musu an zo ana aunawa ba kuma tare da an biya su kuɗin gonakin nasu ba.
Kan wannan batu ne wakilinmu Sanusi Shu'aibu Musa, ya tuntuɓi Daraktan wayar da kai na Ma'aikatar Ƙasa da Tsare-tsare ta jihar Kano, Murtala Shehu Umar, ta wayar tarho, inda ya ce ci gaba ne ya zo wa masu ƙorafin kasancewar awon igiya ne guraren ya sa gwamnatin ta zo da tsari mai kyau.



