Sarkin Kano Sanusi ya samu lambar yabo ta girmamawa daga Cibiyar ICSAN a Legas.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya samu lambar yabo ta girmamawa daga Cibiyar Ƙwararrun Sakatarori da Masu Gudanarwa ta Najeriya (ICSAN), a birnin Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa an baiwa Sarkin wannan lambar yabo ne a wani taro da cibiyar ta gudanar a ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026.
Lambar yabo ta Fellowship na daga cikin karramawar da ake bai wa waɗanda suka cancanta bisa ƙwarewa da gudummawarsu a fannonin shugabanci, gudanarwa da aikin ƙwararru.



