Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya naɗa sabbin dagatai 3 a jihar

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya naɗa Alhaji Ali Abdullahi, a matsayin sabon dagacin garin Ƙaura goje da ke ƙaramar hukumar Nassarawa.
Kalika Sarkin ya kuma naɗa Alhaji Mukhtar Iliyasu a matsayin sabon dagacin garin Faruruwa a karamar hukumar Takai, da kuma Malam Sulaiman Muhammad a matsayin dagacin garin Laugwanni da ke ƙaramar hukumar Takai.
Jim kaɗan bayan kammala naɗin nasu a yau, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya ja hankalin su da su zauna da al'ummarsu lafiya, tare da mayar da hankali wajen tallafawa harkokin tsaro, da lafiya, da ilimin addini da na zamani.
Wazirin Kano Alhaji Sa'ad Shehu Gidado wanda yayi magana a madadin mai martaba sarkin na Kano, ya umarci sabbin dagatan da su guji hulɗa da ɓata gari, da ɓarayi da kuma masu aikata laifuka.
Da suke jawabi, sabbin dagatan da mai martaba sarkin ya naɗa sun bayyana jindadinsu tare da alƙawarin gudanar da aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.
Wakilinmu na masarautar Kano Shu'aibu Ubale Minshawi ya rawaito cewa, sabbin dagatan da aka naɗa sun bukaci al'ummar su da su ba su cikakken haɗin kai domin samun dama wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.



