Koma Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta gudanar da taron wayar da kan al'umma mahimmancin kalandar Musulunci a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta gudanar da taron wayar da kan al'umma mahimmancin kalandar Musulunci a Kano.

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta gudanar da taron wayar da kan al’umma a kan muhimmancin kalandar Musulunci, wadda gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin samar da ita domin amfanin al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali DanAbba, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan muhimmancin kalandar Musulunci da irin rawar da take takawa wajen tafiyar da harkokin ibada da rayuwar Musulmi.

Sheikh Ali DanAbba ya kuma ce, kalandar Musulunci tana da matuƙar muhimmanci wajen tantance lokutan ibadu da suka haɗa da azumi, da Hajji da sauran muhimman al’amuran Musulunci.

A nasa bangaren, Malam Ibrahim Falaki, wanda ya gabatar da muƙala a wajen taron, ya yi bayani kan tarihin kalandar Musulunci da muhimmancin ta ga al'ummar Musulmi a faɗin duniya.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ƙara fahimtar amfani da kalandar Musulunci, tare da kiyaye lokutan da aka tanada bisa tsarin addinin Musulunci.

Taron da ya gudana ranar Lahadi a babban ɗakin taro na ɗakin karatu da ke nan Kano, (State Library) ya samu halartar al'umma da dama, ciki har da malamai, da ɗalibai, da sauransu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM