Majalisar dokokin Kano ta rushe dokar da ta kafa Hukumar KNUPDA, ta jihar.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin dokar Tsare-tsaren Birane da Kula da Cigaban Gine-gine ta shekarar 2026, wanda ya soke dokar da ta kafa Hukumar tsara Birane da raya Kasa ta Jihar Kano, wato KNUPDA.
An zartar da kudirin ne bayan karatu na biyu da na uku a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata 14 ga Yuli, 2026, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore.
Da yake ƙarin bayani bayan zaman, shugaban masu rinjaye a majalisar, kuma wakilin Dala, Hon. Lawan Hussaini, ya ce sabuwar dokar ta kafa Hukumar Kula da Yankin Birnin Kano (KAMA) da kuma Hukumar Kula da Tsare-tsare da Gina Muhalli ta Kano (KADCA), waɗanda za su gudanar da ayyukansu karkashin Ma'aikatar Filaye da tsarin Birane.
Ya ƙara da cewa hukumomin biyu za su karɓi dukkan ayyukan da KNUPDA ke gudanarwa a baya, da suka hada da kula da gine-gine, bayar da amincewar zane-zanen gine-gine, sabunta birane, tsara ci gaban birane da kuma tabbatar da bin dokokin tsare-tsaren muhalli.
Kazalika yayin zaman, shugaban majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da kwamitin wucin gadi da zai hada gwiwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, domin daidaita ayyukan Ma'aikatar Noma da Ma'aikatar Raya Kiwon Dabbobi.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano, Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, ana sa ran kwamitin zai sa ido kan mika dukkan harkokin kiwon dabbobi, kiwon kifi da sauran ayyukan da suka shafi kiwo daga Ma'aikatar Noma zuwa Ma'aikatar Raya Kiwon Dabbobi, kamar yadda Majalisar ta amince.



