Koma Labarai
Labarai

NDLEA ta cafke matashin da ya ɓoye tarin ƙwayoyi cikin wandon sa a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
NDLEA ta cafke matashin da ya ɓoye tarin ƙwayoyi cikin wandon sa a Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta cafke wani matashi bayan da ta same shi da tarin ƙwayoyi da ya ɓoye su a cikin wandon sa.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook, a ranar Talata 15 ga Yuni, 2026.

A cikin da ya wallafa Maigatari ya ce "Babba da jaka ke nan, amma jakar miyagun ƙwayoyi, wannan shi ake kira da mai laya kiyayi mai zamani, mun cafke shi bayan ya ɓoye miyagun ƙwayoyi a cikin al'aurar sa.”

Sadiq Maigatari ya kuma ƙara da cewa, a biyo su domin ganin cikakken bidiyo a kan matashin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM