Gwamnan Kano Abba Kabir ya baiwa Alhazan Kano Riyal 200 kowannen su a Saudiyya

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya cika alkawarinsa na baiwa kowane Alhajin jihar kyautar kudi Riyal 200, a matsayin Barka da Babbar Sallah.
Rahotanni sun bayyana cewa an fara rabon kuɗaɗen ne a ɗaya daga cikin masaukan Alhazan Kano, da ke birnin Makka na Kasar Saudiyya.
Gwamnatin jihar Kano dai ta ware sama da naira miliyan 266, domin aiwatar da wannan shiri, wanda ya amfani Alhazan Kano sama da 3,600 da suka halarci aikin Hajjin bana da aka gudanar.
Rahotanni sun bayyana cewar Amirul Hajj na Jihar Kano, kuma Mai Martaba Sarkin Gaya, Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, ne ya jagoranci rabon kyautar tare da wasu jami’an gwamnatin jihar, da ke kula da harkokin Alhazai a ƙasa mai tsarki.
Da yake jawabi yayin rabon kudaden, Amirul Hajjin ya bayyana cewa, kyautar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na tallafawa Alhazan ta, tare da sanya musu farin ciki a yayin gudanar da ibadar Hajji da bukukuwan Sallah.
Wasu daga cikin Alhazan da suka amfana da kyautar sun bayyana jin dadinsu da wannan karamci na gwamnatin jihar, inda suka yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawarin da ya dauka tare da nuna kulawa ga Alhazan Kano, kamar yadda kafar TST Hausa ta ruwaito.
Kazalika, Alhazan sun kuma yi addu’ar Allah ya karbi ibadunsu, ya kuma saka wa gwamnatin jihar Kano da alheri, tare da ci gaba da ba ta ikon gudanar da ayyukan da za su amfani al’ummar jihar.



