Rundunar Kossap ta kama matashi Usman ɗan rawar solo kan yi wa ɗan sahu ƙwacen kuɗaɗe a Kano.

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta kama matashi Usman Sulaiman ɗan unguwar Ɗorayi, bisa zargin sa da yi wa wani direban Adai-daita sahu ƙwacen kuɗin aiki naira 16,000, a yankin sabon titin Panshekara.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar a Kano, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM, ya ce bayan samun ƙorafi kan ƙwacen kuɗin da matashin ya yi ne kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya tura jami'an su inda suka kamo shi.
Da yake bayyana nadamar sa matashi Usman Sulaiman, ya ce ƙwayoyi da ke bugarwa da sha ne suke sanya shi yi wa masu baburan adai-daita sahu ƙwace, amma wannan shi ne karo na ƙarshe.
A cewar sa, "Ƙwayar da nake sha ce take saka ni yi wa mutane ƙwace, domin idan nasha hankali na yana gushewa in yi abinda ban sani ba, saboda yadda take sanya mini zafin rai," in ji Usman.
Ya kuma ce mafi yawan lokuta ƙwayar har kasheasa kasuwa take yi a gidan rawa (Solo) domin idan za su yi rawa wani lokacin sai ya kasa yin komai sakamakon ƙwayar da ya sha.
Sai dai ya ce kuɗin da ya ƙwatar wa direban baburin Adai-daita sahun naira dubu biyu ne saɓanin naira 16,000, da ya faɗa, inda ya ce da yardar Allah, wannan shi ne karo na ƙarshe ba zai sake yi wa kowa ƙwace ba.
Kakakin rundunar ta Anti-Phone Snatching Force, Ibrahim Garba Ahmad, ya ce tuni Kwamandan rundunar Nura Salisu Ahmad ya ba da umarni da a miƙa matasan inda ya dace domin ɗaukar mataki na gaba.
Rundunar ta Anti-Phone Snatching Force, da akafi sani da KOSSAP, ta kuma buƙaci iyaye da su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu domin ganin goben su ta yi kyau.



