Koma Labarai
Tsaro

Kiran taron haɗin kan ƙasa zai taimaka wajen dawo da tsaro a Najeriya - Sheikh Ali Ɗanabba

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kiran taron haɗin kan ƙasa zai taimaka wajen dawo da tsaro a Najeriya - Sheikh Ali Ɗanabba

Malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya ce akwai buƙatar gwamnati ta kira taron haɗin kan ƙasa, domin hakan zai taimaka matuƙa wajen dawo da tsaro a faɗin ƙasar.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa Sheikh Ali Ɗan Abba, ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook, a ranar Lahadi 14 ga Yuni, 2026.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara a wasu sassan arewacin ƙasar nan, al'amarin da ke ci gaba da tada hankalin al'umma.

Tuni dai masana ke ta kiraye-kiraye ga shugabanni a ƙasar musamman ma na yankunan arewa, da su ƙara tashi tsaye don ganin an ɗauki matakan da suka dace domin ganin an daƙile matsalar rashin tsaron musamman ta garkuwa da mutane, don neman kuɗin fansa, da kashe mutane da ƴan bindiga ke yi haka siddan.

Ready to PlayDala FM88.5 FM