Ƙungiyar matasan ƴan Jarida ta Kano, ta tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin sawa da na abinci.

Ƙungiyar Matasan Ƴan Jarida ta jihar Kano, ta ce akwai buƙatar masu hali su ruɓanya ƙoƙarin su wajen tallafawa da mazauna gidajen gyaran hali da Kayayyakin sawa da na abinci, da sauran abubuwan da suke buƙata, domin rage musu wani radaɗin rayuwa.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Shugaban Ƙungiyar ta Kano Youth Journalist Forum a Kano, Kwamared Musa Zangina Adam ne ya bayyana hakan, a yayin da suka tallafawa wasu daga cikin mazauna gidan ajiya da gyaran hali na Goron Dutse, a ranar Asabar 4 ga watan Satumba, 2026.
A cewar sa, "Kayayyakin da suka kai wa mazauna gidan sun haɗar da Garin Kwaki kwano 10, Omo 50, da Sabulu 10, sai Sukari kwano ɗaya, abun tsaftar mata (Always Pad) Burodi 15, da dai sauransu, sai kayayyakin sawa na maza da na mata da sauransu," in ji shi.
Shugaban Ƙungiyar da ya samu wakilcin Sakataren tsare-tsare na ƙungiyar Matasan Ƴan Jaridar ta jihar Kano, Adam Abubakar Indallahi, ya ce sun kai wa mazauna gidan gyara halin kayayyakin ne domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.
Ya kuma ce yanzu haka ƙungiyar ta fara shirin gudanar da aikin wayar da kan matasa musamman ma mata a wasu daga cikin makarantun Sakandire da ke jihar nan, kan illar shaye-shayen kayan maye, domin ganin an ƙara daƙile wannan matsalar.
Da yake nasa jawabin, Mataimakin Shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano, kuma Shugaban gidan gyaran hali na Goron Dutse, AC Kafilu Abdullahi Nassarawa, ya ce abin da ƙungiyar ta yi abun a yaba ne, inda ya miƙa godiya a garesu.
AC Kafilu Nassarawa ya kuma ƙara da cewa, yadda shan miyagun ƙwayoyi suke taɓa Ƙwaƙwalwar matasa a halin yanzu, akwai buƙatar a rinƙa ɗaukar tsattsauran mataki a kan dilolin ƙwayar domin ganin an magance wannan matsalar.
Shima a nasa ɓangaren, Kakakin Hukumar Kula da gidajen gyaran halin na jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, ya miƙa godiyar su ga ƙungiyar ta Matasan Ƴan Jarida ta jihar Kano, bisa tallafin da ta kai wa mazauna gidan, in da ya yi addu'ar Allah ya saka musu da alkhairi.



