Kwamitin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu, ya kama mutane 13 da ake zargi da ta'ammali da ƙwayoyi a Kano

Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu, ya fara gudanar da aikin sa na farko, inda ya kama mutane 13 da ake zargi da hannu a shaye-shaye da sauran laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da samamen ne ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Gwadabe, wanda shine Jami'in da ke kula da sashen Anti-Daba na rundunar ƴan sandan Kano, a yankunan Sakatariyar Audu Bako, Kofar Dan'agundi, Filin Mahaha da tsakiyar birnin Kano.
A cewar kwamitin, an kama duka mutanen 13 ne a Sakatariyar Audu Bako da ke jihar Kano.
Daya daga cikin waɗanda aka kama, Muhammad Babale, wanda aka ce yana cikin matsanancin maye, an garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
Wannan samame shi ne na farko tun bayan kafa Kwamitin, Musamman kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafawa domin daƙile shaye-shaye, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma laifukan da ke da alaƙa da su a faɗin jihar.



