Koma Labarai
Tsaro

Gwamnan Zamfara ya ce ba za su taɓa yin sulhu da ƴanbindiga ba a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Zamfara ya ce ba za su taɓa yin sulhu da ƴanbindiga ba a jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da 'yanbindiga ba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da kai musu farmaki har sai sun miƙa wuya ko kuma doka ta yi aiki a kansu.

Babban hadimin Gwamnan, Mukhtar Musa, ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sakatariyar Ƙungiyar 'Yan Asalin Zamfara Mazauna Kaduna.

Ya kuma ce gwamnatin jihar na ci gaba da bai wa jami'an tsaro tallafin kayan aiki da sauran buƙatun da za su taimaka wajen yaƙi da rashin tsaro.

Kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, ya kuma yi kira ga al'umma da su riƙa bai wa hukumomin tsaro bayanan sirri kan duk wani motsi da ake zargi domin ƙarfafa yaƙi da masu aikata laifuka.

A wajen taron, gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da bayar da gudummawar naira miliyan biyar ga ƙungiyar. Haka kuma an raba buhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 guda 280 tare da man girki da taliya ga marasa galihu daga cikin mambobin ƙungiyar.

Shugaban ƙungiyar, Garba Balarabe, ya ce sabon sakatariyar za ta zama cibiyar haɗin kai da walwalar 'yan asalin Zamfara mazauna Kaduna, tare da roƙon gwamnatin jihar ta taimaka wajen samar musu da ofishi na dindindin. Taron ya samu halartar jami'an gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM