Majalisa ta buƙataci gwamnatin Kano ta kai ɗauki a garuruwan Sumaila da Magami bisa faruwar iftala'in ambaliyar ruwa da rusau

Majalissar dokokin Kano ta karɓi ƙudurin gaggawa na buƙatar gwamnatin jihar, da hukumar bada agajin gaggawa ta SEMA da su kai ɗauki garin Sumaila da Magami a ƙaramar hukumar Sumaila, bisa iftala'in ambaliyar ruwa da rusau da ya afkawa garuruwan biyu.
A zaman majalisar na yau, ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Jibril Isma'il Falgore, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Sumaila, Zubairu Hamza Masu ne ya gabatar da ƙudurin.
Zubairu Masu ya ce a halin da ake ciki yanzu mutanen wannan yanki na cikin tashin hankali bisa Iftila'in da ya same su lamarin da ya sa suke buƙatar taimakon gaggawa.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa, ko a makon da ya gabata majalisar ta kafa kwamiti da zai rinƙa lura tare da duba irin wannan iftala'in domin magance shi.



