Lalacewar Titi na haifar mana da ambaliyar ruwa da kawo tasgaro a kasuwancin mu - Ƴan kasuwar Ƙofar Ruwa a Kano

Ƙungiyar ƴan kasuwar Rodi da ke Ƙofar ruwa a ƙaramar hukumar Dala a Kano, ta jaddada buƙatar su ta kai musu ɗauki bisa yadda suke fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon lalacewar titin da ya wuce ta kasuwar inda haka ke kawo tazgaro a kasuwancin su.
Jami'in kula da shige da fice a ƙungiyar ta (Musabiha) Alhaji Hassan Mai Glass Ƙofar ruwa, ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da Dala FM Kano.
Ya ce a duk lokacin da aka yi ruwan sama ƴan kasuwar na shan wahala sakamakon lalacewar titin da kuma rashin magudanar ruwa.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala, da sauran masu ruwa da tsaki, da su kai musu ɗauki a kasuwar ta Ƙofar Rufa, domin samun wani sauƙi.
A cewar sa, "Duk lokacin da aka yi ruwan sama to kuwa ƴan kasuwar da masu zuwa wucewa ta titin suna matuƙar shan wahala bisa yadda ake fuskantar ambaliyar ruwa domin ruwa yana zuwar wa mutane har Gwiwa," in ji shi.
Mai Glass ya ƙara da cewa aƙalla sun shafe sama da shekaru uku suna fama da wannan matsalar ta rashin kyan titin da kuma fuskantar ambaliyar ruwa a kasuwar, a don haka suke kira da a kai musu ɗauki.
A cewar sa, idan ruwan sama ya sakko aka samu ruwan sama to kuwa sana'ar su ta tashi sakamakon yadda ruwan sama yake cika kasuwar, saboda rashin magudanar ruwa da kuma lalacewar titin.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya'u ya ruwaito cewa, Hassan Mai Glass ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran masu hali, da su yi duba a kan ƙananan ƴan kasuwa da ke cikin kasuwar ta Ƙofar ruwa, a tallafa musu domin hakan ka iya ƙara taimakawa matasa wajen bunƙasa kasuwancin su.



