Koma Labarai
Tsaro

Rundunar tsaro ta Anti-Phone illicit drugs/Phone Snaching force ta yaye sabbin jami'ai 250 a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar tsaro ta Anti-Phone illicit drugs/Phone Snaching force ta yaye sabbin jami'ai 250 a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da sha da dillancin kayan maye, ta Anti-Phone illicit drugs/Phone Snaching force ta jihar Kano, ta yaye sabbin jami'ai maza da mata su 250, domin ƙara ƙarfafa tsaro a fadin jihar.

Rundunar ta yaye jami'an ne a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba, 2026, a hedikwatar ta da ke Sharaɗa a Kano, bayan da ta basu horon cikin gida na watanni uku, domin ƙara sanin makamar aiki.

Da yake zantawa da manema labarai, Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya ce yaye jami'an na daga shirin Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na ƙara daƙile faɗan daba, ƙwacen waya da kuma ta'ammali da kayan maye, don ƙara wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar.

A cewar sa, "Yaye jami'an zai ba mu dama wajen ƙara baza jami'an mu lungu da saƙo na jihar Kano, domin farautar ɓata gari, ba tare da nuna tsoro ko shakkun kowa ba, kafin babban yayewa da gwamnatin jihar Kano za ta yi wa dukkan jami'an mu" in ji Nura.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Nura Sharaɗa ya kuma bada tabbacin cewa, za su yi duk mai yiyuwa domin ganin an magance matsalolin faɗan daba, da ƙwacen waya da sha da dillancin kayan maye a faɗin jihar Kano.

Ya kuma buƙaci sabbin jami'an da su kasance masu gaskiya da riƙon amana a yayin gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

Nura Sharaɗa ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara jan ƴaƴansu a jiki, tare da tabbatar da cewa ƴaƴan nasu sun kaucewa aikata miyagun ayyuka, yana mai cewa ba za su saurara wa duk wanda ya shigo hannun su da wani laifi ba.

"Duk wanda ya ce jihar Kano ba za ta zauna lafiya ba, to a faɗa masa shi ne ba zai zauna lafiya ba, kuma duk wanda iyayen sa suka ce jeka ka ga ni, to mu zai gani, don haka matasa su tsaya su yi abinda ya kamace su," in ji Nura.

Jami'an da rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force a Kano, wadda akafi sani da KOSSAP, 250, da aka yaye, sun sha alwashin gudanar da aiki bisa gaskiya da amana, ba tare da nuna tsoro ba.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM