Mu na yabawa da matakan da aka ɗauka a kan wasu Alƙalai da ma'aikatan Shari'a a Kano - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta bayyana goyon bayan ta, tare da yabawa Babbar Jojin jihar Kano, Justice Dije Abdu Aboki, da hukumar da ke kula da harkokin Shari'a ta jihar Kano, bisa matakan da aka ɗauka na ladabtar da wasu ma'aikatan kotuna da aka samu da laifi, kuma ciki har da Alƙalai.
Babban Daraktan Ƙungiyar a Najeriya, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Laraba 8 ga watan Yuli, 2026.
A ranar Litinin 6 ga Yuli, 2026, ne dai Hukumar da ke kula da harkokin Shari'a ta jihar Kano, ta bayyana ɗaukar matakai a kan wasu Alƙalai, da wasu ma'aikatan Shari'a bisa zargin su da hannu a laifin cin hanci a wasu shari'u.
Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ya ce ɗaukar waɗannan matakai ya tabbatar wa da duniya cewa, mutumcin tsarin Shari'a ba abin wasa ba ne, kuma babu wani Alƙali, ko ma'aikatan kotu da suka fi ƙarfin doka, wannan mataki yana nuna gaskiya, da tsoron Allah, da kuma kishin tabbatar da adalci ga talakawan jihar Kano.
A cewar sa, "Shekaru da dama al'umma na kuka kan yadda wasu marasa kishin aikin Shari'a ke lalata martabar kotuna ta hanyar cin hanci, da amfani da muƙami ba dai-dai ba, da kuma zaluntar al'umma, saboda haka ya kamata ɗaukar wannan mataki ya zama darasi ga sauran ma'aikata," in ji shi.
Kwamared Karibu Kabara, wanda yanzu haka yake Ƙasar Qatar, ya yabawa Babbar Jojin Kano, Justice Dije Abdu Aboki, kan matakin da aka ɗauka ba tare da nuna tsoro, da cewar ba za a kare duk wanda aka samu da laifi ba, komai matsayinsa.
A cewar sa wannan shi ne ainihin shugabanci na gari, kuma abinda al'umma suke fata daga shugabannin da aka ɗorawa amanar kare gaskiya da adalci.
Ya kuma yi kira ga sauran jahohin Najeriya, da su yi koyi da wannan mataki, domin ta haka ne za a ƙara tsarkake ɓangaren Shari'a, tare da yaƙi da cin hanci da rashawa, idan kotuna suka kasance masu gaskiya, domin kotu ita ce ƙarshen wajen neman adalci.
Ambasada Ƙaribu Kabara, ya kuma yi kira ga dukkanin Alƙalai, da Magatakardan kotuna, da su ji tsoron Allah, su kiyaye rantsuwar da suka yi kafin su fara aiki, kuma akwai ranar tsayawa a gaban Ubangiji S.W.T, da za su yi bayanin dukkanin aikin da suka yi a nan duniya.
A ƙarshe, ya kuma ce suna tabbatar wa Justice Dije Abdu Aboki, cewa, masu kishin adalci da kare haƙƙin bil'adama suna tare da ita a wanna gagarumin aiki da take yi na yaƙi da cin hanci da rashawa, don dawo da mutumci, da kima, da kuma martabar tsarin shari'a a jihar Kano.



