An ƙi barin wakilan jam'iyya ta su kare min ƙuri'a a zaɓen gwamnan Osun - Ɗan takarar ADC
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a zaɓen gwamna da ke gudana yau a jihar Osun, Najeem Salaam ya yi zargin ƙin barin wakilan jam'iyyar da su kare masa ƙuri'a a bakin Akwatuna' zaɓen da ake yi.
Hon. Salaam ya yi zargin cewa hakan ya faru ne a rumfunan zaɓe da dama a faɗin jihar ta Osun.
Salaam wanda ya isa rumfar zaɓe don kaɗa kuri'ar sa da misalin ƙarfe 10:39 na safe, ya ce ya samu rahotanni da dama da ke bayyana cewa ba a barin wakilan jam'iyyar sa ta ADC, duk da cewa jam'iyyar ta turawa INEC sunayen su kafin zaɓen.
Kafar yaɗa labarai ta Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, Salaam ya kuma ce ya samu wannan rahoto a ƙananan hukumomi 10, inda ya ce gwara ya faɗi abinda ke faruwa ga hukumomin da su ka dace.



