Koma Labarai
Tsaro

Har yanzu ba mu ji matakin da gwamnan Kano ya ɗauka ba a kan mutuwar Inuwa Sharaɗa, kwamandan Anti-Phone Snatching Force - Human Rights

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Har yanzu ba mu ji matakin da gwamnan Kano ya ɗauka ba a kan mutuwar Inuwa Sharaɗa, kwamandan Anti-Phone Snatching Force - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation, ta bayyana mamakin ta kan yadda har yanzu gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gaza ɗaukar mataki kan mutuwar Marigayi Inuwa Salisu Sharaɗa, Kwamandan rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force Kano.

Babban daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Auwal Usman Awareness, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai, ya ce duba da yadda Marigayi Inuwa Salisu Sharaɗa, ya ba da gudummawa wajen yaƙi da ɓata gari bai kamata a wofantar da jinin sa ba.

Idan ba a manta ba a ranar Labara 29 ga watan Oktoba, 2025, ne dai Marigayi Inuwa Salisu Sharaɗa, ya rasa ransa, sanadiyyar tura masa jami'an tsaro har gidan sa da ke Sharaɗa a Kano, domin su kama shi, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sa sakamakon haɗuwa da bugun zuciya.

Sai dai a lokacin jana'izar Marigayin, gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin gudanar da bincike tare da ɗaukar mataki a kan duk wanda aka samu da hannu a mutuwar Inuwa, sai dai Kwamared Auwal Usman, ya kuma ce har yanzu ba a ji matakin da gwamnan ya ɗauka ba.

A cewar Auwal Usman, idan har da gaske gwamnan Kano yake, to kuwa ya kamata a fito a bayyana sakamakon binciken da ma matakin da za a ɗauka a kai, duba da irin gudunmawar da Marigayi Inuwa Salisu Sharaɗa ya bayar a Kano.

Kwamared Auwal Usman ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ya ƙara himma wajen daƙile rikicin faɗan daba da ƙwacen waya da kuma shan kayan maye a jihar nan, domin ƙara wanzar da zaman lafiya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM