Koma Labarai
Labarai

Kamfanin TCN zai katse wutar lantarki a sassan jihohi biyar na Arewacin Najeriya.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kamfanin TCN zai katse wutar lantarki a sassan jihohi biyar na Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa Kamfanin rarraba wutar lantarki na ƙasa (TCN) ya sanar da cewa za a samu katsewar wutar lantarki a wasu sassan jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi da Yobe, har ma da yankin Gazaoua na Jamhuriyar Nijar.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, TCN ya ce katsewar wutar za ta biyo bayan aikin kula da na’urorin tashar rarraba wutar lantarki ta Kumbotso mai ƙarfin kilovolt 330, wanda aka tsara gudanarwa ranar Lahadi 28 ga Yuni, 2026.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu yankuna na ƙasar ke fuskantar ƙarancin wutar lantarki, al'amarin da ke jefa su cikin mawuyacin hali.

Ready to PlayDala FM88.5 FM