Kotun ta fi da gidan ka ta Remasab, ta hukunta gidajen Man MRS, Matrix, da asibitin Almu Memorial, da wasu gurare bisa karya doka

Kotun ta fi da gidan ka ta Hukumar Tsaftar muhalli da Kwashe Shara ta jihar Kano REMASAB, ta hukunta gidan man MRS, da Matrix, da asibitin Almu Memorial, da kuma Otal ɗin Dofin Cave, da sauran wasu wurare, bisa samun su da laifin karya dokar tsaftar muhalli.
Wannan na cikin wata sanarwa da Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abubakar Ahmad, ya aiko wa Dala FM a ranar Talata 28 ga Yuli, 2026.
Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne biyo bayan yadda hukumar Remasab, ta ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da tsaftar muhalli da kare lafiyar al'umma, inda ta gurfanar tare da hukunta wasu kamfanoni da cibiyoyi bisa laifukan karya dokokin tsaftar muhalli na jihar.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da bin ƙa'idojin tsaftar muhalli tare da ingiza kamfanoni da cibiyoyi su rungumi kula da muhalli a faɗin jihar Kano.
Daga cikin waɗanda kotun ta hukunta akwai gidan mai na MRS da ke kan Titin Wudil a ƙaramar hukumar Tarauni.
Sanarwar ta ce an sami gidan man da laifukan samun ciyayi da suka mamaye harabar wurin, rashin tsaftar muhalli, zubar da shara barkatai, tara kayan da ba a buƙata, rashin samar da kwandunan shara na zamani, amfani da na'urar kashe gobara da wa'adinta ya ƙare, toshe magudanan ruwa da kuma yawaitar Ɓeraye.
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma, kotun ta samu asibitin Almu Memorial Hospital, da ke kan Titin Maiduguri, da laifin samun ciyayi da suka mamaye harabar asibitin, zubar da shara barkatai, tara kayan da ba a buƙata, rashin kwandunan shara na zamani, rashin tsaftar muhalli, yawaitar gizogizo da kuma toshe magudanan ruwa.
An yanke wa asibitin hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.
Kotun ta kuma samu gidan mai na Conoil da ke kan Titin Maiduguri da laifukan zubar da shara barkatai, ciyayi sun mamaye harabar wurin, rashin tsaftar muhalli, da rashin kwandunan shara, yawaitar gizogizo, tara kayan da ba a buƙata, da tsayuwar ruwa, zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, da kuma yin bayan gida a fili a cikin harabar gidan man.
Har ila yau, shi ma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.
Haka zalika, shima gidan Matrix Filling Station da ke kan Titin Zariya, kotun ta same shi da laifukan zubar da shara barkatai, samun ciyayi sun mamaye harabar wurin, zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, tsayuwar ruwa, rashin tsaftar muhalli, toshe magudanan ruwa da kuma rashin samar da isassun kwandunan shara.
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.
Kotun ta kuma hukunta Dofin Cave Hotel da ke kan Titin Zariya, bayan an same shi da laifukan zubar da shara barkatai, tara tsofaffin bututu, tsayuwar ruwa da kuma tara kayan da ba a buƙata a cikin harabar otal ɗin. An yanke masa hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.
Hukumar ta REMASAB, ta kuma ce, a samamen da ta gudanar, ta samu Bayco Guest Hotel da ke kan Titin Zariya, shi ma ya fuskanci hukunci bayan an same shi da laifukan zubar da shara barkatai, zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, yawaitar gizogizo da kuma rashin kwandunan shara na zamani.
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.
Haka nan, Midland Cardiology Clinic da ke unguwar Na'ibawa, an same shi da laifukan zubar da shara barkatai, samun ciyayi sun mamaye harabar wurin, rashin tsaftar muhalli, yawaitar gizogizo, zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, yawaitar beraye da kuma toshe magudanan ruwa.
Shi ma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.
Da yake jawabi kan sakamakon aikin, Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad Salisu Khalil, ya sake jaddada ƙudirin hukumar na tabbatar da cikakken bin dokokin tsaftar muhalli a faɗin jihar Kano.
Ya bayyana cewa Kotun Tafi-da-Gidanka ta Hukumar Tsaftar Muhalli na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar al'umma, kiyaye tsaftar muhalli da kuma tabbatar da ɗorewar kyawawan ɗabi'un tsafta.
Dakta Khalil ya yi kira ga kamfanoni, cibiyoyin kiwon lafiya, otal-otal, gidajen mai, cibiyoyin kasuwanci da mazauna jihar da su kula da tsaftar muhallansu, su samar da ingantattun hanyoyin zubar da shara tare da bin dokokin tsaftar muhalli.



