Ƙungiyar AHRCF ta buƙaci gwamnatin Kano ta janye sunan Ibrahim Namadi Dala daga naɗa shi Kwamishina

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam da tallafa wa mabuƙata ta Awareness for Human Right and charity foundation, ta ƙalubalanci gwamnatin Kano, kan aikewa da sunan Ibrahim Namadi Dala, a matsayin wanda za ta naɗa Kwamishina.
Babban Daraktan Ƙungiyar Kwamared Auwal Usman Awareness, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM Kano.
A ranar Laraba 21 ga watan Oktoba, 2026, ne dai Majalisar dokokin Kano, ta karanta sunaye shida da gwamnatin jihar ta aike mata, waɗanda take son naɗawa a matsayin Kwamishinoni, ciki har da Ibrahim Namadi Dala.
Sai dai ƙungiyar ta ƙalubalanci tura sunan Namadi, la'akari da yadda a baya gwamnatin ta sauke shi daga matsayin kwamishina bisa zargin sa da karɓar belin ɗan ƙwata a Kano.
Ƙungiyar AHRCF, ta buƙaci gwamnatin Kano ta janye sunan Ibrahim Namadi Dala daga naɗa shi Kwamishina, saboda laifin da aka zarge shi da shi a baya, mai ƙarfin gaske.
A cewar Awareness, indai da gaske Gwamnatin jihar Kano, ƙarkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, take yi wajen yaƙi da ta'ammali da kayan maye, bai kamata a naɗa mutumin muƙamin Kwamishina ba.
Ya kuma ce tunda kotu ba ta wanke Namadi ba, kuskure ne gwamnatin jihar Kano ta kuma sake bashi wani muƙami, indai za a bi tsarin doka da oda, domin bai cancanci hakan ba.



