Hukumar Shari'a ta gudanar da rangadin faɗakarwa a tashar Mariri da kasuwar Ƴankaba da ke Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta gudanar da rangadi zuwa tashar mota ta Mariri da kasuwar sayar da kayan miya ta Ƴankaba, domin ƙulla alaƙar aiki tare da ƙara duba kan yadda za a kawo tsafta a cikin al'amuran al'umma a faɗin jihar nan.
Hukumar ta gudanar da ran gadin ne a ranar Alhamis, domin faɗakar da ƴan kasuwa da kuma direbobin mota, a kan tanadin addinin musulunci a harkar kasuwanci da kuma cuɗanya da al'umma, tare da kawo tsafta da magance matsaloli a faɗin jihar Kano.
Ziyarar na daga cikin shirin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, na ƙara kawo ci gaba da daƙile sha da dillancin miyagun ƙwayoyi da kuma ƙara tsaftace al'amura a faɗin jihar nan.
Da yake ƙarin bayani, Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce sun kai ziyarar tashar mariri ne domin jan hankalin direbobi wajen kula da amana da kuma kaucewa cuɗanya da masu shigo da miyagun ƙwayoyi da sauran kayan lefe Kano.
Sheikh Ɗanabba ya kuma ƙara da cewa, a yayin ziyarar da suka kai kasuwar sayar da kayan miya ta Ƴankaba, sun gana da shugabancin kasuwar da ma ƴan kasuwar, inda suka faɗakar da su kan yaɗi da miyagun ƙwayoyi da ma ƙara tsaftace kasuwancin su.
Da yake nasa jawabin, mataimakin shugaban kasuwar sayar kayan miya ta Ƴankaba a Kano, Sabo Jika, ya ce dama tuni suka ɗauki gaɓarar yaƙi da ɓata gari domin ƙara tsaftace kasuwar don ci gaban al'ummar Kano.
Shima a nasa ɓangaren, Shugaban ƙungiyar tashar mota ta mariri ɓangaren ƴan Tasi, Bilya Sa'adu Kawu, ya ce a shirye suke wajen amfani da faɗakarwar da hukumar shari'ar ta yi musu, domin ganin an gudu tare an kuma tsira tare.
Tunda farko da yake nasa jawabin, Kwamishina na ɗaya a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Gwani Muhammad Tahir Yakasai, ya buƙaci shugabannin ƴan kasuwar da su ƙara tsawatarwa da mambobin su wajen ganin sun kaucewa cutar da kwastomomi.
A yayin ziyarar, Kwamishinonin hukumar sun samu rakiyar daraktoci, da wasu shugabannin hukumar Shari'ar ta jihar Kano.



