Gwamnonin Arewa ku ƙara ninka ƙoƙarin ku don daƙile matsalar tsaro a yankin - Human Rights

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na Kano, Kwamared AA Haruna Ayagi, ya bayyana cewar matsalar tsaron da ake fuskanta a jihar Kano, da wasu sassan Najeriya, na buƙatar hannun al'umma domin daƙile ta.
Kwamared AA Ayagi, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Network a Najeriya, ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da Dala FM Kano.
A cewar sa, "Matsalar garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa ta zama tamkar ruwan dare musamman a Arewacin Najeriya, da kuma faɗace-faɗacen daba a birane da matasa suka tsunduma, a wasu yankunan Kano, da ma sassan wasu jahohin ƙasa, in ji Ayagi.”
Ya kuma ce akwai buƙatar gwamnonin Arewacin Najeriya su ƙara ninka ƙoƙarin su domin ganin an daƙile wannan matsala.
"Tabbas ba za a fita daga matsalar tattalin arziƙi ba matuƙar akwai matsalar tsaro a ƙasa, in ji shi.”
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Kwamared Ayagi ya kuma buƙaci al'ummar ƙasa da su sanya hannu wajen kai wa jami'an tsaro rahoto da zarar sun ga wani abu wanda ba su yarda da shi ba, domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.



