Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta ce nan gaba kaɗan za ta sanar da ƴan takarar da ya kamata a zaɓa a 2027

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewacin Najeriya ta ce nan gaba kaɗan za ta fito ta bayyana ƴan takarar shugaban ƙasa da jahohi da ƴan majalisu da ya kamata a zaɓa, a babban zaɓen 2027.
Shugaban ƙungiyar Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano, jim kaɗan bayan ƙaddamar da ƙungiyar.
Muhammad Tijjani ya ce manufar ƙungiyar ita ce, yadda za su tunkari yadda arewa ke fuskantar matsaloli musamman na tsaro, da lokaci yayi da al'ummar wannan yanki za su fito don kawo ƙarshen su, ta hanyar fitowa su zaɓi cancanta a lokacin zaɓe.
Sai dai MTD, ya ce, ƙungiyar ta lura da cewa yanzu an fara samun nasara wajen yaƙi da ta'addanci a sassan Najeriya, la'akari da yadda hukumomin tsaro ke ƙara ƙarfafa tsaro a ƙasar.
Ya kuma ce za su tabbatar da al'umma sun zaɓi mutanen da suka cancanta a babban zaɓen 2027, kuma waɗanda za su amfanar da ƴan Najeriya.
A cewar sa, kan hakan ne ma ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa, nan gaba kaɗan za ta gudanar da gangamin wayar da kan al'umma a kan mahimmancin zaɓen waɗanda suka cancanta a zaɓen 2027.



