Koma Labarai
Tsaro

Ƴan Sandan Kano sun kama mutane 345 cikin kwanaki 3 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan Sandan Kano sun kama mutane 345 cikin kwanaki 3 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa, ta samu nasarar kama mutane 345 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, a wani samame da ta gudanar a fadin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai, a ranar Litinin 8 ga Yuni, 2026.

A cewarsa, "Samamen ya gudana ne daga ranar 5 zuwa 7 ga watan Yuni, inda aka mayar da hankali kan wuraren da ake zargin masu aikata laifuka ke maboya da kuma wuraren da ake ta’ammali da miyagun kwayoyi, in ji shi.”

CP Bakori ya ce daga cikin abubuwan da aka kwato akwai makamai masu haɗari guda 270 da suka haɗa da wuƙaƙe, adduna da gatari, tare da miyagun kwayoyi iri daban-daban.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kan waɗanda aka kama, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Ready to PlayDala FM88.5 FM