Koma Labarai
Labarai

Hukumar PCACC ta fara bincikar tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano Abdullahi Musa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar PCACC ta fara bincikar tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano Abdullahi Musa

Hukumar ƙarɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta fara gudanar da bincike a kan tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Musa.

Rahotanni daga hukumar sun nuna cewa, a na binciken Abdullahi Musa kan zargin sa da cire kuɗi daga albashin ma’aikatan gwamnati ba tare da amincewarsu ba.

Majiyoyin sun ce jami’an hukumar sun je gidan tsohon shugaban ma’aikatan da ke rukunin gidaje na Almukab City da ke Karamar Hukumar Kumbotso, inda suka yi rubutu a jikin ƙofar gidan da cewar ana bincike ʼUnder Investigationʼ tare da sunan PCACC da kwanan wata 18 ga Mayu 2026.

Hukumar ta kuma ce ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma ɗaukar matakan da suka dace idan an tabbatar da zargin da ake yi.

Ready to PlayDala FM88.5 FM