Gwamnatin Kano a ɗauki mataki kan yadda ake neman cutar da mutane 1,163, kan ɗaukar aiki a jihar - Human Right

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network a Najeriya, ta buƙaci gwamnatin jihar Kano, da ta yi gaggawar bincike tare da ɗaukar mataki kan yadda aka yi zargin an karɓe takardun ɗaukar aiki (Offer Permanent and Pensionable Appointment) a fannin koyarwa a makarantun lafiya, tun gabanin su fara aiki.
Babban Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ne ya bayyana hakan bayan da suka karɓi ƙorafi daga wajen wasu daga cikin malaman da ake shirin yi wa ta leƙo ta koma a kan aikin da aka basu.
A cewar sa, "Aƙalla malamai 1,163, ne gwamnatin jihar Kano ta baiwa takardun ɗaukar aiki da za su koyar a makarantun kiwon lafiya, amma daga bisani aka kirawo su aka karɓe takardun ba tare da sun fara aiki ba, wanda yanzu haka ake ƙokarin soke batun ɗaukar aikin ma gaba ɗaya abinda ya jefa su cikin damuwa," in ji shi.
Ambasada Ƙaribu Kabara, ya ce yanzu haka akwai tarin waɗanda aka karɓe takardun ɗaukar aikin da suka shigar da ƙorafin su a babban ofishin ƙungiyar, domin a shige musu gaba kan lamarin.
A cewar sa, bayan da suka karɓi ƙorafin mutanen ne ƙungiyar ta Global Community for Human Rights Network, ta rubuta takardu zuwa ga ofishin Shugabar Ma'aikatan jihar Kano, Hajiya Bilkisu Mai Mota, domin jin ba'asi kan zargin soke ɗaukar aikin ga mutane 1,163, domin gujewa take haƙƙin mutanen.
Kabara ya kuma ce, a takardun da suka turawa ofishin Shugabar Ma'aikatan, suna buƙatar bayanan a kan ingancin takardun ɗaukar aikin da aka baiwa mutanen a baya aka karbe, shin suna da inganci ko akasin hakan, tunda an bayyana takardun ɗaukar aikin (Offer Permanent and Pensionable Appointment) sun fito ne daga gwamnatin Kano.
Ya kuma ce bayan ofishin Shugabar Ma'aikatan Kano, sun rubuta takardun zuwa ga ofisoshi guda biyar (5), da suka haɗar da Gwamnatin Kano, da Anti Corruption, Civil Service, Technical Board, domin sanar da su a kan wannan matsalar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin ta kuma buƙaci gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya yi gaggawar ɗaukar matakan da suka dace a kan wannan al'amari, domin tabbatar da adalci ga mutanen da ake shirin takewa haƙƙi.
A cewar Ambasada Ƙaribu Kabara, wannan abu ka iya cutar da siyasar gwamnan Kano, da kuma gwamnatin sa, tare da kawo wa Kano, talauci da ƙara haifar da masu zaman banza a gari, da kuma aikata laifuka, idan har aka soke batun ɗaukar mutanen aiki har su 1,163, a jihar Kano.
Ya zama wajibi Gwamnatin jihar Kano, ta ɗauki matakan da suka dace a kan wannan al'amari matukar da gaske ne tana kishin al'ummar ta, da kuma kare martabar su, domin baiwa mutanen aiki ka iya taimaka wa wajen rage rashin aikin yi a tsakanin matasa da ma sauran al'ummar jihar.



