Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano a ƙara yawan ajujuwan makarantun karkara da na birni - Human Rights

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano a ƙara yawan ajujuwan makarantun karkara da na birni - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights ta jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin Kano da ta ƙara ajujuwa a makarantun ƙananan hukumomin yankunan karkara, domin daƙile cunkoson ɗalibai a cikin aji, tare da samun ingantaccen ilimi.

Daraktan ƙungiyar a nan Kano, Kwamared Umar Sani Galadanci ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM a ranar Litinin 30 ga Yuni, 2026.

Ya kuma ce yadda mafi yawan makarantun sakandare da Firamare ke fuskantar kalubale akwai buƙatar gwamnatin Kano, ta ƙara himma wajen magance su.

Umar Galadanci ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta ƙarfafa tsaro a makarantu musamman ma na karkara domin daƙile mummunar manufar masu kawo tazgaro a harkar tsaro.

A ƙarshe Galadanci ya yi fatan gwamnati za ta yi wa shawarwarin su kyakkyawar fahimta tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen magance waɗannan matsaloli, domin ƙara bunƙasa ilimin ɗalibai a jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM