Koma Labarai
Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta ce za ta iya sake buɗe binciken tsohon mataimakin gwamna Comrd. Aminu Gwarzo

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar Dokokin Kano ta ce za ta iya sake buɗe binciken tsohon mataimakin gwamna Comrd. Aminu Gwarzo

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore, ya ce majalisar na da ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta na sake bude bincike kan zargin karkatar da kudade da ake yi wa tsohon Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, idan buƙatar hakan ta taso.

Jibril Ismail Falgore ya faɗi hakan ne ta cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon Kano.

Falgore ya ce ko da yake an dakatar da binciken ne bayan Gwarzon ya yi murabus daga mukaminsa, hakan ba ya hana majalisar komawa kan lamarin a nan gaba idan ta ga ya dace.

Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Falgore ya kuma bayyana cewa an ware ayyukan mazaɓu da kuɗinsu ya kai naira miliyan 500, ga kowane ɗan majalisar domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a mazaɓunsa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM