Koma Labarai
Labarai

Hisbah ta sanya ranar fara yi wa waɗanda za su ci gajiyar auren gata gwajin lafiya a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hisbah ta sanya ranar fara yi wa waɗanda za su ci gajiyar auren gata gwajin lafiya a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce za a fara yi wa waɗanda suka cike Form, domin neman gurbi game da auren gata da gwamnatin Kano za ta yi wa mutane dubu uku a jihar.

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Lahadi 7 ga Yuni, 2026.

Gwamnatin jihar Kano ce dai ta shirya yin auren gatan ga mutane dubu uku, domin saukaƙa musu wajen yin auren, a wani ɓangare na auren gata da za a yi musu.

A cewar sa, "Hukumar mu ta yi haɗin gwiwa ne da Ma'aikatar Lafiya ta jihar Kano, domin yi wa waɗanda za su ci gajiyar auren gatan gwajin lafiyar, in ji shi”.

Dr. Mujahideen ya kuma ce aƙalla al'ummar ƙananan hukumomin wajen Kano, 24 ake buƙata domin yi musu gwaje-gwajen lafiyar a ranar Litinin 8 ga watan Yuni, 2026.

Ƙananan hukumomin da ake buƙatar zuwa wajen gwajin sun haɗar da Rogo, Wudil, Tudun Wada, da Warawa, da kuma Kibiya, sai Dawakin Tofa, da Garun malam, Kura, da Dambatta da kuma Ƙaraye.

Sauran sun haɗar da Tsanyawa, Minjibir, Rimin Gado, Shanono, da Kabo, da kuma Tofa, Rano, sai Bebeji, Ajingi, da Gwarzo, Sumaila, da Kiru, da kuma Takai, da Madobi.

Dr. Aminudden ya ƙara da cewa duk wanda ya tsallake gwajin lafiyar shi ne zai samu gurbi na auren gatan, na mutane dubu uku da gwamnatin Kano za ta yi, ƙarkashin jagorancin Hukumar Hisbah ta jihar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM