ICPC ta sake bankaɗo wasu sabbin hukumomin bogi guda biyu a yayin binciken PFIPC a Najeriya.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar yaki da ayyukan rashawa a Najeriya ICPC, ta bankaɗo wasu sabbin hukumomin bogi guda biyu, yayin da take bincike kan hukumar bogi ta PFIPC.
Shugaban hukumar ICPC Dr Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka, yayin da yake gabatar da rahoton bincike ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda kafar DCL ta ruwaito.
Ya kuma ce binciken nasu ya gano cewa Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC Prince Adeyemi Adeniyi ne ya kirkiri sabbin hukumomin biyu.



