Matar da ta ƙirƙiri sanarwar cewa Opay zai daina aiki ta shiga hannun jami'an Ƴan Sandan Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ‘yansandan Najeriya ta kama matashiya Hafsat Abubakar, mai shekara 27, bisa zargin ta da ƙirƙira da yaɗa wata takardar bogi da ke cewa kamfanin OPay zai daina aiki.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, ya fitar, ya ce an kama Hafsat ne ranar 4 ga Satumba 2026, bayan kamfanin OPay, ya kai ƙorafi ga rundunar ‘yansanda a ranar 31 ga Agustan 2026.
Ya kuma ce cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ‘yansanda ta gudanar da binciken ƙwaƙƙwafi na Internet, inda aka gano cewa takardar ta samo asali ne daga wani shafin X da Hafsat Abubakar ke amfani da shi.
A cewar ƴansandan, "Takardar ta bogi ce kuma an gabatar da ita tamkar sanarwar hukuma daga OPay, inda ta yi ikirarin cewa kamfanin zai dakatar da ayyukansa daga 1 ga watan Satumba, 2026," in ji sanarwar.
Kamfanin na OPay ya musanta sanarwar, yana mai cewa kamfanin na ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Rundunar ‘yansandan ta yi gargadin cewa yaɗa bayanan bogi ta kafafen sada zumunta na iya haifar da firgici, da matsalar kuɗi da kuma ɓata sunan kamfanoni.
Kafar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, rundunar ƴan sandan ta kuma buƙaci jama’a da su rinƙa tabbatar da sahihancin muhimman bayanai daga majiyoyin hukuma kafin su yaɗa su.



