Gwamnatin Kano ta dakatar da buɗe "Film House" a unguwar Ɗorayi
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani gini da ake zargin za a mayar da shi gidan wasan kwaikwayo (Film House) a unguwar Ɗorayi Karama, cikin Unguwar Bello, da ke Karamar Hukumar Gwale a jihar Kano.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan rufe ginin, shugaban kwamitin kar-ta-kwana na daƙile gine-ginen da aka yi ba bisa ka'ida ba, kuma shugaban riko na Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano, Dakta Ɗalhatu Aliyu Sani, ya ce wurin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai gwamnati ta kammala nazari kan lamarin.
Wakilinmu Abba Isa Muhammad, ya rawaito cewa, kwamitin ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da bibiyar duk wani gini da aka dakatar ko ake gudanar da shi ba bisa ka’ida ba, domin ɗaukar matakin da ya dace.



