Kotu ta aike da mutumin da ake zargi yana sojan gona da sunan ɗansanda gidan yari a Kano.

Kotun majistret mai lamba 53 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Jamilu Ɗayyabu Haruna, ta fara sauraron wata Shari'a wadda yansanda suka gurfanar da wani mutum mai suna Musa Adamu, wanda ake zargi da laifin sojan gona da cuta.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, mutumin yayi sojan gona da sunan cewar shi babban sifirtanda ne na yansanda, (CSP)
An kuma zargi cewa mutumin yana karɓar kuɗi a hannun mutane da zummar zai samar musu aiki.
A zaman kotun na ranar Alhamis 10 ga watan Satumba, 2026, yayin da aka karanta masa zarge-zargen ya musanta.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, kotun ta sanya shi a hannun beli amma sai ya kawo mutum mai matakin albashi na 15 idan kuma ya tsere za a biya dubu ɗari biyar.
Kotun ta sanya ranar 28 ga watan Satumba, 2026, domin ci gaba da sauraron shari'ar.



