Majalisa ta ƙara karɓar kudirin buƙatar ɗaukar mataki kan matsalar tsaron da ta addabi Ƙauyen Ƴan kamaye da ke Tsanyawa, Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano ta karɓi kudirin gaggawa a kan matsalar tsaro da ke ƙara tsamari a garin ƴan kamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar.
Ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙananan hukumomin Ghari da Tsanyawa Garba Ya'u Gwarmai, ne ya gabatar da ƙudurin a zaman majalisar na ranar Talata 21 ga Yuli, 2026.
Ya'u Gwarmai ya ƙara da cewa, ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa kan wannan matsala, kasancewar wannan shi ne karo na biyu yana gabatar da wannan ƙuduri.
Kazalika ya bayyana cewa, akwai kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomi da suka shafi matsalar tsaro, sai dai kawo wannan lokacin jami'an tsaron na cigaba da kokawa.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano, Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, shugaban majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya buƙaci kwamitin kananan hukumomi da masarautu da ya bincika tare da gabatar da rahoton sa cikin makonni biyu.



