Ɓata gari sun kashe Yahaya mai shayi a Ƙofar Nasarawa, Kano, bayan caka masa Ɗanbida

Wasu ɓata gari sun kashe wani magidanci da ke sana'ar sayar da Shayi mai suna Mallam Yahaya, a unguwar Ƙofar Nassarawa da ke jihar Kano.
Shaidun gani da ido sun shaidawa Dala FM Kano, cewa, ɓata garin sun biyo Marigayin ne cikin daren ranar Litinin 13 ga Yuli, 2026, lokacin da ake ruwan sama daga yankin Ƙofar Nassarawa, inda suka cimmasa a yankin gidan Zoo suka caka masa Ɗanbida lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Ma'ajiyar ta kuma bayyana cewa, ɓata garin sun kuma ɗauke baburin Marigayin mai ƙafa biyu, inda suka gudu da shi.
Mazauna unguwar Ƙofar Nassarawa da kewaye sun buƙaci jami'an tsaro da su ƙara tsaurara sintiri a yankunan su, musamman ma daga ƙarfe tara na dare zuwa sallar Asuba, domin daƙile matsalar.
Sun buƙaci hakan ne duba da yadda wasu ɓata gari suke amfani da lokutan cikin daren wajen yi wa mutane fashin baburan hawa a titunan yankunan, lamarin ma da ya yi sanadiyyar kashe mai shayin Mallam Yahaya.



