Koma Labarai
Siyasa

Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta ce har yanzu Pantami ɗan jam'iyyar ta ne.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta ce har yanzu Pantami ɗan jam'iyyar ta ne.

Jam’iyyar APC, ta ƙasa reshen jihar Gombe, ta jaddada cewa tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Ali Pantami, har yanzu mamba ne na jam’iyyar, tana mai cewa ba a bi ƙa’idojin da suka dace wajen ficewarsa daga jam’iyyar ba.

Sakataren yaɗa labarai na APC a jihar, Moses Kyari, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai.

Ya ce shugabannin APC na mazaɓar Pantami sun tabbatar da cewa ba su karɓi ko tattauna wata takardar murabus daga gare shi ba.

"Aƙalla mambobi 25 cikin 27 na kwamitin gudanarwar mazabar sun yi watsi da ikirarin cewa Pantami ya fice daga APC, suna mai cewa labarin ƙirƙirarre ne, in ji shi.”

Kyari ya kuma ƙara da cewa shugaban mazabar, Bala Galda, ya ce an karɓi takardar murabus ɗin ne a ranar 23 ga Mayu, duk da cewa an rubuta ta ranar 19 ga watan, kuma wani Abba Pantami ne ya kai ta. Ya ce har yanzu ba a nuna wa mambobin kwamitin kwafin takardar ba.

Kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, a cewarsa, bisa kundin tsarin APC, ƙa’idojin INEC da Dokar Zaɓe, Pantami zai ci gaba da kasancewa mamba a APC har sai an kammala dukkan matakan da doka ta tanada.

Jam’iyyar ta kuma musanta ikirarin da ake cewa Pantami ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na TVC cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da sauya sheƙarsa zuwa PDP da kuma takararsa ta gwamna. APC ta ce ba za a yi tunanin shugaban ƙasa zai goyi bayan wani mataki da zai iya raunana haɗin kan jam’iyyar ba.

APC ta kuma yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Yahaya kan abin da ta kira nasarori a fannonin mulki, samar da ababen more rayuwa da tabbatar da zaman lafiya a jihar, tare da kira ga shugabannin APC na ƙasa da fadar shugaban ƙasa su fito su fayyace gaskiyar lamarin domin kauce wa yaɗa bayanan da ka iya rikitar da jama’a.

Ready to PlayDala FM88.5 FM